Rikici ya Kaure a Jahar Kaduna, Mutane 30 Sun Rasa Rayukansu
Aƙalla mutum 30 suka mutu sannan an kona gidaje da dama a kauyukan Madamai da Abun na karamar hukumar Kaura da ke jahar Kaduna.
Read Also:
Jaridar Daily Trust ta rawaito tsohon shugaban kungiyar hadin-kan matasan Kaura, Kwamared Derek Christopher na cewa maharan sun kutsa yankunan da misali karfe 5 na yamma suka rinka harbe-harbe kan mai uwa dawabi.
Ya kuma shaida cewa yawancin mutanen da aka jikkata an kai su asibiti domin basu kulawa.
Rundunar ‘yan sanda Kaduna kawo yanzu ba ta ce komai a kan harin ba.