Magance Matsalar Tsaro: Janar Irabor na Neman Dabaru da Taimakon Manyan Sojojin da Sukai Murabus

 

Shugaban ma’aikatan tsaro, Janar Leo Irabor, ya ce akwai bukatar sojoji su nemi dabaru da kwarin guiwa daga sojojin da suka yi murabus don samar da zaman lafiya a kasa.

Ya yi wannan furucin ne yayin jawabi a wani taro na manyan sojoji da suka yi murabus na yankin arewa ta tsakiya da aka yi a Makurdi.

Irabor ya bukaci sojojin da suka yi ritaya da kada su dauka cewa sun kammala ayyukansu, face suma suna da rawar takawa a harkar tsaro.

Makurdi, Benue – A ranar Laraba, Shugaban ma’aikatan tsaro na Najeriya, Janar Leo Irabor, ya ce sojoji suna bukatar samun dabaru da kwarin guiwa daga sojojin da suka yi murabus don cigaban kasa.

Daily Trust ta ruwaito cewa, ya yi wannan furucin ne yayin jawabi a wani taron karawa juna sani na manyan sojojin Najeriya na yankin arewa ta tsakiya da suka yi a Makurdi.

Sojoji suna daa wuka da nama na kawo karshen rashin tsaro

A cewarsa, sojoji sunada damar da zasu kawo karshen duk wasu rashin tsaro da suke addabar kasa, amma ya bukaci sojoji masu murabus da kada su sare ko su yi tunanin sun fita daga cikin masu baiwa kasa tsaro, hasalima su amince da cewa suna da ruwa da tsaki a harkar tsaro.

A cewar Irabor:

Don tabbatar da zaman lafiya a kasar nan, muna bukatar neman dabaru daga manyan sojoji wadanda suka yi murabus. Saboda sun yi aikin nan kuma suna da dabaru da masaniya akan yadda ake shawo kan matsalar tsaro.

Matsawar ka taba zama soja, har abada kai soja ne ko da kana aiki ko kayi murabus. Babban burin kasar nan shine samun zaman lafiya, kwanciyar hankali da natsuwa kuma mun yi rantsuwa akan tabbatar da hakan kuma za mu yi iyakar kokarinmi, a cewarsa.

A jawabin CDCIMIC, Rear Admiral Frederick Ugo, ya bayyana muhimmancin tattunawa tsakanin sojoji masu murabus da masu aiki a halin da kasa ta tsinci kanta, Daily Trust ta ruwaito.

A cewarsa:

Mun samu horarwa mai yawa, ilimi da dabaru na musamman a hannunsu. Suna da salon gano hanyoyin shawo kan matsalar tsaro saboda tunaninsu da namu zai banbanta.

Wajibi ne mu hada karfi da karfe wurin shawo kan matsalar rashin tsaro.

Dama AOC, AVM Idi Lubo, a nashi jawabin ya bayyana imaninsa akan tabbas akwai wani lamari mai kyau da zai zo nan kusa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here