Gwamnatin Iraƙi ta Kama Jigon Kungiyar IS
Gwamnatin Iraki ta kama wani babban kusa a kungiyar Islamic State (IS) da ake zargi da kula da harkokin kudinta.
Firaministan Irakin Mustafa al-Kadhimi ya bayar da sanarwar kama Sami Jasmin, yana mai cewa an gudanar da aikin mai sarkakiya a wajen ƙasar ta Iraki.
Ya kuma bayyana Jasim a matsayin tsohon mataimakin shugaban kungiyar IS Abubakar al-Baghdadi da sojojin Amurka suka kashe shekara biyu da suka gabata.
Wakilin BBC ya ce a shekarar 2005 ne sojojin Amurka suka kama shi har zuwa 2010 inda suka sake shi.
Sai dai a 2015 Amurka ta yi shelar bayar da lada ga duk wanda ya taimaka mata wajen sake kama Jasim.
Sai dai duk da shan kayen da kungiyar ta yi na rasa yankunan da ke karkashin ikonta a 2017, har yanzu tana ci gaba da kai hare-hare a kasar ta Iraki.