Firaiministan Isra’ila ya yi Barazanar ƙwace Yankunan Gaza
Firaiministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya sake yin barazanar karɓe yankunan Gaza, muddin Hamas ba ta saki sauran mutanen da take garkuwa da su ba.
Mista Netanyahu ya shaida wa majalisar dokokin ƙasar cewa, zai ƙara matsin lamba ga ƙungiyar ta Hamas.
Read Also:
A wata sanarwar da Hamas ta fitar, ta ce a duk lokacin da Isra’ilar ta yi ƙoƙarin ƙwato mutanen da take garkuwan da su, sai dai ta karɓo gawarsu.
Inda ta ƙara da cewa sabbin hare-haren da take kaiwa ta sama, na ƙara jefa rayukan waɗanda ake garkuwar da su cikin haɗari.
Jami’an lafiya na Falasɗinawa sun ce, fiye da falasɗinawa 800 aka kashe tun bayan da Isra’ila ta koma kai hare-hare mako guda daya wuce.