Dakarun Isra’ila Sun Kai Hari Cibiyar Raba Tallafi ta Rafah – MDD
Hukumar kula da ‘yan gudun jihirar Falasɗinawa ta Majalisar Dinkin Duniya UNRWA ta ce an kashe ɗaya daga cikin ma’aikan hukumar tare da raunata wasu mutum 22 a lokacin da dakarun Isra’ila suka kai hari cibiyar raba tallafin abinci a Rafah, da ke kudancin Zirin Gaza.
Read Also:
Shugaban hukumar ta UNRWA, Philippe Lazzarini ya ce hare-hare kan cibiyoyin hukumar, ya ”zama saɓo dokokin ayyukan jinƙai na duniya ne”.
A wani labarin kuma ma’aikatar lafiyar Hamas da ke Gaza ta ce hare-haren dakarun Isra’ila ta sama sun kashe mutum biyar
Kawo yanzu dai rundunar sojin Isra’ila ba su ce komai ba game da batun.
Yankin Rafah dai na cike da Falasɗinawan da aka ƙiyasta cewa sun kai miliyan 1.4, da ke neman mafaka daga hare-haren dakarun Isra’ila ta ƙasa daga wasu wurare a Gaza.