Aƙalla Falasɗinawa 85 ne Suka Rasa Rayukansu a Sabon Hare-Haren Isra’ila
Aƙalla Falasɗinawa 85 aka kashe a hare-haren cikin dare da Isra’ila ta kai kan Gaza, kamar yadda ma’aikatar lafiyar Hamas ta shaida.
Sa’oi bayan nan rundunar sojin Isra’ila ta ce ta kakkaɓo wasu jiragen roka uku da Hamas ta ce ta harba a Tel Aviv.
Lamarin ya zo ne bayan da Isra’ila ta koma yin luguden wuta a zirin cikin makon nan, inda hare-haren suka kashe fiye da mutum 430 cikin kwana biyu da suka gabata, a cewar ma’aikatar lafiyar.
Read Also:
Rundunar sojin Isra’ila, IDF ta ce ta soma kai farmaki ta ƙasa a arewacin Gaza. An ɗan samu raguwar kai hare-hare tun watan Janairu lokacin da yarjejeniyar tsagaita wuta ta soma aiki.
Isra’ila ta koma kai hare-hare a ranar Talata yayin da tattaunawar tsawaita yarjejeniyar ta fuskanci cikasa, inda ta yi gargaɗi cewa za su zafafa hare-hare har sai Hamas ta saki ragowra mutanen da take tsare da su.
Isra’ila ta ce har yanzu Hamas tana riƙe da mutum 59, wasu 24 kuma ana tunanan suna nan da ransu.
Kakakin IDF, Kanar Avichay Adraee ya ce Hamas ta harba rokoki uku daga kudancin Gaza. An kakkaɓo ɗaya daga cikinsu, sauran biyun kuma suka faɗa wani fili, kamar yadda ya wallafa a shafin X.