Isra’ila za ta Halarci Taron Tsagaita Wuta Kan Yaƙin Gaza
Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu ya ce zai aika wakilai zuwa birnin Rum na Italiya, domin halartar taron tattauna batun tsagaita wuta a yaƙin Gaza.
Mista Netanyahu ya bayyana hakan ne a lokacin ganawarsa da tsohon shugaban Amurka, kuma ɗan takarar shugaban ƙasar a jam’iyyar Republican, Donald Trump a wata ziyara da yake yi a Amurkan.
Read Also:
Furucin firaministan Isra’ilan na zuwa ne kwana guda bayan tattauna batun tsagaita wutar yaƙin a ganawarsa da shugaba Biden da wadda ke fatan yi wa jam’iyyar Demokrats takarar shuagabancin ƙasar, Kamala Harris.
Gwamnatin Biden ta ce Isra’ila da Amurka na ƙoƙarin kawo ƙarshen yaƙin.
Misis Harris ta ce ba za ta yi ”shiru” game da batun ba, ganin yadda mazauna Gaza ke ”wahala”, inda ta yi kira ga duka ɓangarorin biyu su cimma matsaya.