Mun Dade Muna Harba Roka Sansanin Sojoji Dake Mallam Fatori a Jahar Borno – ISWAP

 

Mayakan ISWAP wadanda aka fi sani da Boko Haram sun yi ikirarin jefa roka a garin Mallam Fatori a jahar Borno.

‘Yan ta’addan sun kai wa sansanonin sojoji farmaki sakamakon harin har suna hallaka sojoji 5 a garin.

An samu wannan bayanin ne a wata takarda ta ranar 1 ga watan Satumba wacce ISWAP ta fitar.

Mallam Fatori, Borno – Mayakan ISWAP wadanda aka fi sani da Boko Haram sun harba roko zuwa Mallam Fatori da ke jahar Borno har sau hudu a cikin mako daya tak.

Daily Nigerian ta rawaito yadda ‘yan ta’addan sun kai wa sansanonin farmaki a harin wanda ya yi sanadiyyar salwantar sojoji 5.

A wata takarda wacce IS ta saki a ranar 1 ga watan Satumba, ‘yan ta’addan ISWAP sun ce sun dade suna harba roka sansanin sojoji da ke Mallam Fatori kuma sun hallaka sojoji 4 kenan tun ranar 25 daga watan Augusta.

“Ubangiji Allah ya bai wa sojoji masu jahadi nasara akan sansanin sojoji cikin kwana biyu da suka gabata a garin Mallam Fatori da ke jahar Borno, sakamakon harba rokar Katyusha.

“Kuma ta isa inda muka aikata, mun gode wa Allah,” kamar yadda takardar da suka saki a ranar 2 ga watan 2 na Satumba wacce Daily Nigerian ta gani ta ce.

A ranar 2 ga watan Satumba, kungiyar ta saki hotuna 6 wadanda suke nuna mayakan suna harba roma fa sansanin sojojin garin da suka bayyana.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here