‘Yan Ta’addan ISWAP Sun Kai Hari Garin Ajiri Dake Jahar Borno

 

‘Yan ta’addan ISWAP sun kai mugun farmaki garin Ajiri dake karamar hukumar Mafa a Borno.

Sun kai harin ne a ranar Lahadi amma har yanzu ba a san iyakar barnar da suka yi ko aka musu.

A watan Augustan da ta gabata ne ‘yan gudun hijira suka koma Ajiri da taimakon gwamnatin jahar.

Mayakan ISWAP, wani bangare na Boko Haram da suka rabe, a ranar Lahadi sun kai mugun farmaki yankin Ajiri dake karamar hukumar Mafa ta jahar Borno.

Harin da aka kai Ajiri ya sa an fara damuwa da halin tsaron da garin Dikwa zai shiga a kwanakin nan.

Mafa tana daya daga cikin kananan hukumomin jahar Borno da gwamnatin jahar ke ta zuba kudi domin gina gidaje saboda dawowar ‘yan gudun hijira. Har yanzu dai ba a sani ba ko an samu tsayyayun sojoji da aka tura yankin, jaridar HumAngle ta wallafa.

A kalla an samu gidaje 500 da ‘yan gudun hijira suka koma a Ajiri a watan Augustan 2020 tare da taimakon gwamnatin jahar da ta samar musu da gidajen, kayan abinci da tallafin kudi.

HumAngle ta gano cewa a ranar Asabar, 1 ga watan Mayu ne dakarun sojin Najeriya suka fatattaki mayakan ISWAP da suka shiga garin Rann, hedkwatar karamar hukumar Kala Balge dake da kusanci da Kamaru. Mayakan ta’addancin sun isa a motocin yaki da babura inda aka gano cewa sun matukar jigata bayan arangamarsu da dakarun.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here