‘Yan Ta’addan ISWAP sun Kai Hari Barikin Sojoji a Jahar Yobe

‘Yan ta’addan ISWAP sun kai hari barikin Sojojin Kumuya dake jahar Yobe ranar Asabar, 17 ga Afrilu, 2021 inda suka lalata manyan makaman hukumar Soji.

Yan ta’addan sun kai harin kwantan baunan ne lokacin jami’an 27 Task Force Brigade da aka tura Buni Gari sun fita sintiri.

PRNigeria ta tattaro cewa yan ta’addan sun dira Kumuya ne tare da taimakon yan gari da masu leken asiri.

Hakazalika an tattaro cewa Sojojin da ake wajen sun yi musayar wuta da yan ta’addan suka suka samu galaba kansu. Kawo yanzu ba’a san adadin wadanda suka rasa rayukansu ba amma Sojoji sun tare hanyar Damaturu-Damboa-Biu.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here