Kungiyar ISWAP Sun Kai Sabon Hari a Rann Dake Jahar Borno

 

Kungiyar ISWAP ta kaddamar da wani gagarumin sabon hari a Rann, hedkwatar karamar hukumar Kala Balge a jahar Borno, Daily Trust ta rawaito.

Bayanai sun ce mazauna garin da yawa sun tsere zuwa Kamaru sakamakon wannan harin.

Rann gari ne a jahar Borno dake da iyaka da kasar Kamaru.

An ce mayakan dauke da muggan makamai sun kutsa cikin garin da sanyin safiyar Litinin 30 ga watan Agusta, 2021.

Har yanzu ba a samu wasu cikakkun bayanai game da harin ba, amma an ba da rahoton sun kona gidaje da yawa tare da yin artabu da musayar wuta da sojoji.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here