‘Yan Ta’addan ISWAP Sun Kashe Kwamandan Shekau

Rahotannin da ke iso mu sun nuni da cewa, ‘yan ta’addan ISWAP sun hallaka kwamandan Shekau a cikin dajin Sambisa.

Wannan na zuw ane bayan da ‘yan ta’addan suka gano yana shirin tuba tare da mika kansa ga sojojin Najeriya.

A baya dai wannan jigon kusa da Shekau ya hada kai da ISWAP ne bayan da shugabansu Shekau ya mutu.

Borno– Rahotanni sun bayyana cewa ‘yan ta’addar Boko Haram da ISWAP sun kawar da daya daga cikin manyan kwamandojin su Abu-Sadiq wanda aka fi sani da Burbur bisa zarginsa da shirin mika wuya ga dakarun gwamnati.

Jaridar Leadership ta tattaro cewa an kashe Burbur ne a kauyen Galta da ke kusa da Madagali bayan tuhumarsa da laifin cin amana a wata kotun ‘yan ta’adda ta Ya-Shaik, ISWAP Fiye na dajin Sambisa.

A cewar wani rahoton sirri da aka samu daga majiyar soji ta bayyana cewa, Bubur ya kasance a gidan yari na ISWAP a watan Afrilu bayan da aka kama shi hannu dumu-dumu yana shirin mika kansa ga soji.A karshe an kashe shi a ranar 9 ga Mayu, 2022.

Batun na fitowa ne daga kwararre kan harkar yaki da tsaro Zagazola Makama a birnin Maiduguri.

Abubuwan da ya kamata ku sani game Burbur

Majiyar ta ce kafin rasuwarsa, Burbur ya kasance mataimakin shugaban tsageru, mai kula da dajin Sambisa da kusurwowi uku na Timbuktu.

An nada shi ne a watan Mayun 2021 lokacin da ya yi mubaya’a ga ISWAP, saboda saninsa sosai game da yankin da kuma dabarunsa na baya a matsayin kwamandan ayyukan ta’addanci a mafakar marigayi Abubakar Shekau.

Burbur ya kasance mai kula da kai hare-hare a sansanonin sojoji da garuruwa da suka hada da Michika, Madagali, Askira Uba da sauran sassan jihar Adamawa.

A matsayinsa na daya daga cikin amintattun mashekin dan ta’adda marigayi Abubakar Shekau, an sha ganin Bubur na tsaye a baya da fagen Shekau a cikin faya-fayan bidiyo.

Sauran manyan kwamandojin Shekau DA suka yi mubaya’a ga ISWAP sun hada da Ba’a Umara, Ba’ana Biga, Abu Maryam, Abu Ayuba, da Ibn Yusuf.

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here