2020: Abubuwan da Suka Jawo Matsalar Tattalin Arziki a Najeriya
A shekarar 2020 ne Najeriya ta sake shiga cikin matsijn lambar tattalin arziki
Coronavirus da cire tallafin man fetur sun taimaka wajen jawo wannan matsi .
Masana suna ganin akwai hannun karancin Dalar Amurka da karyewar Naira.
Jaridar The Cable tayi bincike game da yadda annobar COVID-19 da rufe iyakokin kasa da aka yi suka jawo tashin farashi da karancin kudin shiga a 2020.
Alkaluman CPI wanda suke auna sauyin da ake samu a farashin kaya ya tashi sosai a shekarar 2020. NBS mai tattara alkaluma na kasa ta tabbatar da haka.
Tashin farashin kaya da aka rika samu a shekarar da ta wuce ya kara jefa al’umma cikin matsin talauci kamar yadda Ministar kudi, Zainab Ahmed ta bayyana.
Read Also:
Gwamnatin tarayya ta bada umarnin a rufe duka iyakokin kasa a watan Agustan 2019, da nufin hana shigowar makamai da miyagun kwayoyi cikin Najeriya.
A shekarar baran an yi ta fama da hare-hare a gonakin Bayin Allah, wannan ya jawo kayan abinci da masarufi suka kara kudi, farashin kaya su ka zabura a kasuwa.
Masana suna kuma alakanta tsadar kayan abincin da aka samu da karyewar darajar Naira da takunkumi wajen samun kudin kasar waje da tsadar kudin mai.
Cire tallafin man fetur da karin kudin shan wutar lantarki da aka yi a cikin shekarar 2020 ya sake jagwalgwala abubuwa ta yadda harkar kasuwanci ya kara wahala.
Daga cikin abubuwan da suka haddasa matsalar tattalin arziki a Najeriya, akwai annobar nan ta cutar Coronavirus wanda ta addabi mafi yawan kasashen Duniya.
Masana tattalin arzikin kasar suna ganin cewa za a cika da fama da wadannan matsaloli a 2021.