Wasu Jahohi Zasu Samu Matsalar Wutar Lantarki
Babbar tashar wutar lantarki ta lalace, kuma hakan zai kawo cikas ga wutar lantarkin wasu jihohi.
Jihohin da rashin wutar zai shafa sun hada da jihar Kaduna, Sokoto, Kebbi da jihar Zamfara.
Shugaban yada labarai na kamfanin rarrabe wutar lantarki na jihar Kaduna ya sanar da hakan.
Abdulazeez Abdullahi, shugaban yada labarai na kamfanin rarrabe wutar lantarkin jihar Kaduna, ya tabbatar da aukuwar wani lamari a wata takarda da ya gabatar ranar Lahadi, The Cable ta wallafa.
Kamar yadda ya wallafa a shafinsa na kafar sada zumuntar zamani ta Twitter, Abdullahi ya sanar da lalacewar tashar samar da wutar lantarki ta kasa, da misalin karfe 11:26 na safiyar Lahadi.
Read Also:
Kamar yadda ya wallafa, “Muna masu takaicin sanar muku da za ku fuskanci rashin wutar lantarki a jihar Kaduna, Sokoto, Kebbi da jihar Zamfara, sakamakon lalacewar tashar rarrabe wutar lantarki ta kasa. Al’amarin ya faru ne da misalin karfe 11:26 na safe.”
“Za mu yi kokarin tabbatar da gyarawa cikin gaggawa. Muna fatan za a gafarcemu.”
Haka kuma kamfanin rarrabe wutar lantarki na Eko, (EKEDC) sun tabbatar da lalacewar tashar wutan, har suka tura wa mutane sako a ranar Lahadi.
“Muna masu takaicin sanar da ku lalacewar tashar wutar lantarki ta kasa, za a fuskanci rashin wuta na wani lokaci.
“Muna yin iyakar kokarin gyaran TCN din mu don samar da wutar lantarki. A gafarcemu,” yace