Jahohin da Za su Amfana da NEDC
Ma’aikatar NEDC ta ce ta dauki dawainiyar horas da sama da mutane 2, 000.
Mutanen Gombe, Taraba, Bauchi sai Borno, Adamawa da Yobe za su amfana.
Wasu matasan za su samu damar yin karatun Digirin farko, Masters da PhD Ma’aikatar NEDC ta ce wasu mutanenta daga yankin Arewa maso gabas za su amfana da tsare-tsaren da aka shigo da su domin inganta rayuwar jama’a.
A ranar Litinin NEDC da aka kafa domin cigaban Arewa maso gabas ta ce ta ware Naira biliyan shida domin wannan aiki a karkashin tsarin NEDC-EEF.
Jaridar This Day ta rahoto babban jami’in ma’aikatar tarayyar, Malam Abba Musa ya na cewa NEDC za ta dauki dawainiyar ilmin mutane fiye da 2, 000.
Abba Musa ya ce NEDC za ta tura yara 2, 056 da za su yi karatu a makarantun gaba da sakandare.
Read Also:
“Za a dauki nauyin karatun yara da za su samu digirin farko, na biyu da na uku a fadin jihohin Arewa maso gabas; mutane 2, 056 daga gudumomi 1, 028.”
“Mutane 336 daga kananan hukumomi 12 na bangaren jihohin Arewa maso gabas za su samu damar yin digirgir a jami’o’in Najeriya da na kasashen ketare.”
Ya ce: “Mutum 18 za su amfana da damar yin karatun Digirin PhD daga mazabu 18 na yankin.”
“Za a dauki mutane 5, 000 masu karamin karfi kamar marayu da karatunsu ya tsaya a sanadiyyar rikicin Boko Haram da za a koya masu wasanni.” Inji Musa.
Ma’aikatar ta ce wannan tsari zai bada dama ta musamman ga mutane 2000 da ke karatun gaba da sakanadare, ta yadda mutane 20, 000 za su amfana a shekara.
Dazu kun ji cewa Najeriya ta na jiran Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sa hannu a kundin kasafin k
Jihohin da za su amfana da NEDC su ne; Gombe, Taraba, Bauchi sai Borno, Adamawa da jihar Yobe.