Najeriya: Jahohin da Suka fi Yawa da Kamuwa da Cutar Korona

Gwamnatin tarayya ta bayyana jihohi uku da suka debi kaso mafi yawa wadanda suka kamu da cutar Korona a Najeriya.

Acewar kwamitin fadar shugaban kasa na yaki da COVID-19, jihohin sune Legas, Abuja da Kaduna.

Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, ya bayyana dalilin da ya sa hakan ya faru.

Yayinda ake tsoron sake kakaba dokar kulle karo na biyu a fadin Najeriya, gwamnatin tarayya ta bayyana Legas, Kaduna da Abuja matsayin manyan cibiyoyin kamuwa da Korona.

Boss Mustapha, Sakataren gwamnatin tarayya, ya bayyana hakan ranar Litnin, 21 ga Disamba, a Abuja yayin hira da manema labarai, ThisDay ta ruwaito.

A cewar shugaban kwamitin PTF, wadannan jihohin ne suka kwashi kashi 70% na adadin masu Korona a Najeriya.

Kawo ranar Litinin, hukumar hana yaduwar cututtuka a Najeriya (NCDC) ta tabattar da cewa adadin wadanda cutar Korona ta kama a Najeriya na gab da 80,000.

Boss Mustapha ya ce ummul haba’isin hauhawar adadin masu kamuwa da cutar Korona ba komai bane illa taruwan jama’a, da kuma watsi da dokokin kare kai da hukuma ta gindaya.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here