Hukumar NECO ta Bayyana Jahohin da Aka fi Yin  Magudin Jarabawar

 

Jahar Kano, Bauchi da Bauchi sun fito zakaru cikin jahohin da ake mugun magudin jarabawa.

Daliban sakandare na zana jarabawar NECO kowace shekara don kammala karatunsu.

Shugaban NECO ya gabatar da jawabi kan yadda za’a magance matsalar satan jarabawa.

Abuja – An bayyana jahar Bauchi, Kano da Kebbi a matsayin jahohin da ake mumunar magudin jarabawar kammala karatun Sakandare a Najeriya.

Shugaban hukumar Jarabawar kasa, NECO, Dantani Wushishi, ya bayyana haka, rahoton Punch.

A cewar Wushishi,

“A 2016, alkaluman magudin jarabawa sun nuna Bauchi na 8.17%, Kaduna 6.20%, Kano 5.51%, Plateau 5.31%, da Sokoto 8.87%.

“A 2017, Bauchi (10.79%), Kebbi (16.06%), Borno (7.87%) da Kano (7.29%).”

“A 2018, Kano (12.45%), Kebbi (10.71%), Gombe (5.40%) da Zamfara (5.14%).”

“A 2019, Bornu (13.08%), Kano (11.70%), Kebbi (8.67%), Taraba (5.04%) and Yobe (6.56%)”

“Hakazalika a 2020, Adamawa (18.51%), Bauchi (7.88%), Kaduna (6.87%), Kano (7.88%) da Katsina (18.01%).”

Wushishi ya ce a shekaru biyar da suka gabata, Bauchi, Borno, Kano da Kebbi akafi samin satar jarabawa a Najeriya.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here