Jahohin da Suka fi Yawan Motoci a Najeriya
Cikin motoci miliyan 13 da ke hawa a titunan Najeriya, kashi 50 cikin 100 da ke wakiltar miliyan 6.5 ana hawansu ne a jahohin Legas da Kano, jahohi biyu mafiya karfi a fanin kasuwanci a ƙasar.
Yayin da ake bayyana Legas na cibiyar kasuwancin Najeriya, jahar Kano ta kasance cibiyar kasuwanci arewacin Najeriya.
Jaridar Leadership ta rawaito kwamishinan hukumar inshora ta kasa, Mista Sunday Thomas ya ce Kano na jan ragama wajen abubuwa da dama a Najeriya, yana jadada cewa Kano da Legas kawai ke hawa kashi 50 cikin 100 na motoci Najeriya.
Ya ce akwai bukatar Kano ta yi aiki da su wajen yi wa ababen hawa inshora, hakan zai taimaka wajen sake haɓɓaka kuɗaɗen shigarta.