Jami’ar Kashere ta Jahar Gombe ta Kori Dalibai 23
Jami’ar Kashere ta gwamnatin tarayya a jahar Gombe ta kori wasu dalibanta bisa wasu dalilai.
Wannan na zuwa ne daga hukumomin jami’ar inda suka bayyana dalilin korar daliban nasu.
Hakazalika, jami’ar ta sanar da cewa, nan kusa za a fara karatun samester na gaba na kalandar bana.
Gombe – A ranar Talata ne Jami’ar Tarayya ta Kashere da ke jahar Gombe ta sanar da fatattakar wasu dalibanta 23 daga makaranta sakamakon laifin ta’ammuli da jabun sakamako da kuma ta’annuti a jarrabawa.
Jami’an jami’ar sun kuma amince da dakatar da dalibi daya na wucin gadi, Daily Nigerian ta rawaito.
Wannan batu na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban yada labarai da hulda da jama’a a jami’ar, Suleiman Malami ya fitar, ranar Talata 5 ga watan Oktoba a jahar Gombe.
Read Also:
Malami ya ce matakin ya biyo bayan shawarwarin da majalisar dattijai ta jami’ar ta yi yayin taronta na 68 na yau da kullum da ya gudana a makon jiya.
Punch ta nakalto shi yana cewa:
“Majalisar Dattawan Jami’ar a taronta na 68 na yau da kullum da aka gudanar a ranar 23 ga Satumba, 2021 ta yi la’akari da amincewa da korar su da tsatstsaura mataki kan aikin su nan take.”
Mista Malami ya ce an gano daliban da aka koran suna son buga jabun sakamakon jarrabawa da barna a jarrabawa.
An kusa dawowa karatu a jami’ar
Sanarwar ta kuma nakalto Kabiru Garba-Aminu, magatakardar jami’ar yana cewa an kammala shirye-shiryen dawowar dalibai cikin kwanciyar hankali na kalandar ilimi ta semester ta biyu ta 2020/21.
Mista Garba-Aminu ya yi kira ga iyaye da su tabbatar da cewa ‘ya’yan su sun dawo makaranta a kan lokaci saboda za a fara karatu nan take.
Ya sake nanata kudirin mahukuntan jami’ar na samar da yanayi mai kyau na koyo don tabbatar da ba a sami matsala a zangon ba.
Magatakardar ya kuma bukaci al’ummomin da ke zagaye da jami’ar da su ba da hadin kai da goyan bayan gudanarwa da kuma daliban.