Jami’an Tsaro Sun Kama Shugaban Majalisar Dokokin Filato da aka Tsige, Abok Ayuba

Rahotanni daga jahar Filaton Najeriya na cewa jami’an tsaro sun kama shugaban majalisar dokoki da aka tsige Alhamsi din da ta gabata, da kuma wasu yan majalisa 10 da ke goyon bayansa.

Jaridun cikin gida sun ruwaito cewa yan sanda sun isa zauren majalisar da misalin karfe 3:15 na rana, kuma ba tare da wata-wata ba suka yi awon gaba da honorabul Abok Ayuba da yan koren nasa su 10.

Wasu rahotannin sun ce jami’an tsaro sun bade masu bore a harabar majalisar dokokin da hayaki mai sa hawaye.

An ambato dan majalisa mai wakiltar Langtang ta Kudu Honorabul Zinghtin Sohchang yana fada wa yan jarida cewa “gamu nan jami’an tsaro sun tura mu cikin mota kirar Hilux kuma bamu san ina za a je damu ba.”

A makon da ya gabata ne yan majalisar dokokin jihar Filato suka tsige shugaban majalisar Abok Ayuba, wanda aka dade ana hasashen cewa basa ga maciji da gwamna Simon Lalong.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here