Jami’an Tsaro Sun Kama yan Ta’adda a Abuja

 

FCT, Abuja – Jami’an rudunar yan sandan kasar nan ta bankado maboyar yan ta’adda a yankin Sauka, a hanyar tashar jirgin sama da ke Abuja.

Yan sandan sun yi nasarar kama wasu masu garkuwa da mutane, ciki har da wani tsohon mai laifi Yau Sani, da Nuhu, sai Kabiru Muhammed da Yusuf Hassan.

FCT Police Command ta wallafa a shafinta na X cewa kakakin rundunar yan sandan Abuja, SP Josephine Adeh ce ta tabbatar da yan ta’addan na daga cikin bata-garin da su ka addabi mazauna Abuja.

Yadda aka gano maboyar yan ta’adda

Jaridar Leadership ta wallafa cewa kakakin rundunar yan sandan Abuja, SP Josephine Adeh ta bayyana cewa a ranar zagayowar yancin kan kasar nan ne aka gano maboyar yan ta’addan.

Ta ce bayan jami’ansu sun samu rahoton sirri kan ayyukan yan ta’addan ne su ka bibiye su har aka kai ga gano inda su ke.

Yan ta’adda sun amsa laifin satar jama’a

Rundunar yan sandan kasar nan ta bayyana cewa mutane hudu da aka kama a Abuja sun amsa laifin satar mutane da dama a Abuja da kewaye.

Matasan hudu sun ce sun kai hare-hare yankunan Dakwa, Dawaki, Rukunin gidajen Aco, Dupe Village Zuma Rock, kauyen Kuchiko da wasu kauyukan a jihohin Kaduna da Neja.

Haka kuma an yi nasarar kwato bindigar AK-47 da alburusai da dama daga hannunsu.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here