Sunayen ‘Yan Shia’a 6 da Jami’an Tsaro Suka Kashe a Zaria

 

Shugaban Kungiyar IMN ta Zaria ya bayyana sunayen mambobinsu wadanda suka rasa rayukansu a tattakin Ashura a Zaria.

Kamar yadda ya bayyana, akwai Jafar Jushi, Kazeem Magume, Ali Samaru, Muhsin Zakzaky, Umar Fatika da wani daya da ba a gano sunansa ba.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna, DSP Mohammed Jalige ya tabbatar da faruwar lamarin amma yace yana jiran cikakken rahoton.

Zaria, Kaduna – A ranar Litinin, 8 ga watan Augustan shekarar 2022 ne Musulmai mabiya addinin shi’a suka fito kwan su da kwarkwata domin yin tattakin muzahharar Ashura.

Sai dai cike da rashin sa’a, an samu arangama tsakanin mabiya Shi’an da tawagar jami’an tsaro a Zaria dake jihar Kaduna inda aka rasa rayukan ‘yan shi’a har shida yayin da wasu suka jigata.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa, a wata takaitacciyar sanarwa da IMN ta fitar na yadda lamarin ya faru, sun ce arangamar ta faru ne yayin da ‘yan kungiyar suka fito nuna bakin cikin Ashira a Zaria.

“Jami’an tsaro a yau Litinin, sun bindige mana mabiya a kalla shida kuma sun raunata kusan 40 daga cikinmu yayin tattakin Ashura a Zaria, wanda muka yi shi cikin lumana a fadin Najeriya da sassan duniya,” takardar tace.

Hakazalika, shugaban IMN na Zaria, Abdulhamid Bello, ya zargi cewa tawagar hadin guiwa ta jami’an tsaro sun dinga harbi babu kakkautawa kan mambobinsu.

Sunayen wadanda suka rasa rayukansu Bello ya bayyana sunayen wadanda aka kashe a Zaria kamara haka:

Jafar Jushi

Kazeem Magume

Ali Samaru

Muhsin Zakzaky

Umar Fatika da kuma wani wanda har yanzu ba a gano sunansa ba.

A yayin da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna, DSP Mohammed Jalige, yace ya san da faruwar lamarin amma har yanzu ba a kawo masa cikakken bayani ba.

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here