Jami’an Ukraine 300 ne Suka Rasa Rayukansu a Harin da Rasha ta Kai Birnin Mariupol

Mun sami karin bayanai kan harin sama da dakarun Rasha suka kai a birnin Mariupol na kudancin Ukraine.

Kawo yanzu, ba a san yawan wadanda suka mutu daga harin ba saboda ci gaba da kai hare-hare babu kakkautawa da sojojin Rasha ke yi kan birnin.

Amma jami’an Ukraine a yanzu sun ce kimanin mutum 300 ne suka rasa rayukansu yayin wancan harin, wanda ya fada kan wani ginin gidan wasannin kwaikwayo, inda daruruwan ‘yan Ukraine ke neman mafaka.

Jami’an Ukraine na cewa Rasha ce ta kai harin, sai dai Rashar ta musanta ikirarin nasu.

Ofishin Magajin Garin Mariupol ya ce “Daga bayanan da shaidu suka sanar da mu, kimanin mutum 300 ne suka halaka a ginin Drama Theatre na Mariupol wanda ya biyo bayan hare-hare da jiragen yakin Rasha suka kai.”

Sai dai kafofin sadarwa da birnin na Mariupol sun kasance ‘yan kalilan, saboda haka ne babu yadda za a iya tantance sahihancin rahotannin da ke fitowa daga can.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here