Bayan Harin ‘Yan Bindiga: Jami’an Tsaro Sun Tsananta Sintiri a Jahar Zamfara
Rundunar ‘yan sandan jahar Zamfara da wasu hukumomin tsaro sun tsananta sintiri a Zamfara.
An samu bayanai kan cewa miyagun ‘yan bindiga za su kai farmaki wasu yankunan Tsafe na jahar.
Jami’an tsaron sun bukaci mazauna yankin da su samar musu da ingantattun bayanai domin shawo kan matsalar.
Tsafe, Zamfara – ‘Yan sandan jihar Zamfara da wasu jami’ai daga hukumomin tsaro da suka hada da sojoji sun tsananta sintirin sama da kasa a yankin Gusau zuwa titin Tsafe zuwa Yankara dake karamar hukumar Tsafe ta jahar.
Read Also:
Daily Nigerian ta ruwaito cewa, wannan na kunshe ne a wata takarda da mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jahar, SP Muhammad Shehu ya fitar a Gusau.
Cikakken bayanin jami’an tsaro
Akwai rahotannin sirri da suka bayyana cewa ‘yan bindiga na barazanar kai hari wasu yankunan karamar hukumar Tsafe dake jahar.
Rundunar tare da hadin guiwar wasu hukumomin tsaro ballantana sojojin sun tsananta tsaro a Tsafe da kewaye domin baiwa dukiyoyi da rayuka tsaro,”‘yan sandan suka ce.
Ana kira ga jama’a da su kwantar da hankalinsu tare da ci gaba da ayyukan su.
Ana karawa da kira ga jama’ar yankunan da su samar da ingantattun bayanai ga hukumomi na ayyukan ‘yan bindigan domin daukar mataki,” yace.