Gwamnan Kano: Wata Jami’ar Kasar Amurka ta Karrama Gaduje

Jami’ar ‘East Carolina’ da ke kasar Amurka ta aikowa gwamna Ganduje takardar daukansa aiki a matsayin Farfesa.

A cewar Jami’ar, iliminn Ganduje, kwarewa a mulki, da shaidar kirki da aka yi masa sune silar daukansa aikin.

Idan har ya amince da bukatar Jami’ar, Ganduje zai shiga sahun manyan malamanta da ke aiki a cibiyar ECU-ICITD.

ECU-ICITD, wata cibiyar bunkasa fasahar sarrafa labarai ta kasa da kasa a Jami’ar East Carolina da ke kasar Amurka, ta dauki gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, aiki a matsayin Lakcara.

Jami’ar ta dauki Ganduje a matsayin babban masani da ke matakin Farfesa wanda zai ke koyar da darussan ‘E-Governance’ da ‘International Affairs’ a bisa tsarin malami mai ziyara.

Jami’ar ta ce ta zabi karrama Ganduje da wannan aiki ne domin samun damar karuwa da dumbin iliminsa, basirarsa, da kwarewa a harkar mulki.

Wani bangare na takardar daukar aiki da jami’ar ta aikowa Ganduje na cewa, “za mu ji dadi a ce koda sau daya ne a shekara za ka samu damar yin magana da dalibanmu a wurin taron bita da karawa juna sani.

“Idan har za mu fadi gaskiyarmu, mun zabeka ne saboda dumbin iliminka, kwarewar aiki, da tarihin iya jagoranci a Najeriya da nahiyar Afrika, hakan ya sa ka zama mutumin da jami’ar ‘East Carolina’ ke nema domin cimma muradanta a matsayin cibiyar bayar da ilimi a kasar Amurka da duniya baki daya.

A karshen wasikar, jami’ar ta bayyana cewa; “mu na fatan za ka karbi wanna aiki, ya mai girma. Da zarar mun samu takardar amincewarka, za mu saka sunanka cikin jerin manyan malamanmu a cibiyar ECU-ICITD.”

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here