Jami’ar Nnamdi Azikiwe za ta Kori Dalibai da Malamai Bisa Aikin Assha
An samu wata mummunar barna a jami’ar gwamnatin tarayya da ke jihar Anambra a kwanan nan, an yi kokarin gyara komai.
Ya zuwa yanzu, an bayyana yadda malaman jami’a suka yi aikin assha a jami’a tare da karbar kudin dalibai haka siddan.
Ana yawan samun lokuta da dama da ake korar malaman jami’a a Najeriya biyo bayan karbar rashawa da cin hanci daga dalibai.
Awka, jihar Anambra – Tashin hankali ya dabaibaye Jami’ar Nnamdi Azikiwe da ke Awka a jihar Anambra, yayin da wani kwamitin ya ba da shawarar korar wasu mutane sama da 14 da suka hada da ma’aikata da dalibai bisa wasu laifuffuka.
Wadanda abin ya shafa sun hada da wani malamin addini da malaman boko uku, tare da karin daliban da za su fuskanci kora saboda laifuka daban-daban, rahoton The Nation.
Read Also:
Wannan bayanin ya fito ne a cikin wata sanarwa a hukumance mai dauke da sa hannun Dr Emmanuel Ojukwu, mashawarci na musamman ga shugaban jami’ar a fannin hulda da jama’a, inda yaba manema labarai a Awka a ranar Lahadi, 24 ga watan Satumba.
Yadda batun ya faru
Ku tuna cewa shugaban Jami’ar Farfesa Charles Esimone, ya sha kokawa kan wani babban kalubale da ya shafi cin zarafi da badala da sauran laifuka daban-daban a jami’ar.
An zargi wasu malamai guda uku da karbar kudade daga hannun daliban da suka yi nasarar kammala karatunsu, lamarin da yake haramun a jami’a.
A bangare guda, ana zargin wani rabaran din coci da wani mutum da laifin taimakawa barna da aikata rashin da’a tare da karbar rashawa daga dalibai.
Malami ya gyara ‘carryover 12’ ga dalibai
Ana kuma zargin daya daga cikin malaman makarantar da laifin goge faduwar wasu dalibai tare da bari su kammala baya ga faduwa a kwasa-kwasai 12.
Kwamitin ya ba da shawarar a kore shi daga aikin jami’a, tare da janye sakamakon da ya ba daiban, sannan a hana ba da kammala karatu garesu.
Ba sabon abu bane samun yanayi irin wannan a Najeriya, kuma jami’o’i da gwamnati na daukar matakin da ya dace.