Jam’iyyar PDP ta yi Martani Kan Shugaba Buhari

 

A ranar Alhamis, jam’iyyar adawa ta PDP ta yi wa shugaba Buhari wankin babban bargo.

Jam’iyyar ta ce shekaru 5 kenan Buhari yana mulkin Najeriya amma ya gaza tsinana komai.

Ta ce Buhari ba zai iya fuskantar ‘yan majalisar tarayya bane saboda ba zai iya kare kansa ba Jam’iyyar PDP ta yi wa Buhari kaca-kaca a ranar Alhamis.

Ta ce ya kasa tabuka komai cikin shekaru 5 da yake kan karagar mulki, The Punch ta wallafa.

Kamar yadda sakataren yada labaran PDP, Kola Ologbondiyan yace, Buhari bashi da abinda zai cewa ‘yan majalisar tarayya, shiyasa ba zai iya amsa gayyatarsu ba.

A cewarsa, “Shugaban kasa a tsorace yake, bashi da abinda zai fada wa ‘yan Najeriya a kan matsalar tsaro.

Wannan yasa yake ta kame-kame, ya tsere yaki fuskantar ‘yan majalisar. Ya kasa yin komai tun da ya hau mulki, ciki har da bayar da tsaro.”

Kakakin jam’iyyar PDP ya kara da cewa, babu wani shiri da ‘yan majalisar tarayya, ‘yan jam’iyyar PDP suka yi don tozarta shi a taron yau.

Tsoro ne kawai ya kama shugaba Buhari. Ologbondiyan ya fadi hakan ne a ranar Alhamis, yayin da ake tattaunawa da shi a wani shiri na gidan talabijin a Legas.

Dama makon da ya gabata, majalisar tarayya, wacce Femi Gbajabiamila yake jagoranta, ta gayyaci shugaba Buhari don tattaunawa da shi a kan matsalar rashin tsaro, sakamakon kashe-kashen manoman Zabarmari 45 da aka yi a jihar Borno.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here