Gwamnatin Sokoto Zata Kafa Kungiyar Hisbah

 

Gwamna Tambuwal na jihar Sokoto ya shirya tsaf don kirkirar hukumar Hisbah da zata rage ayyukan bata gari ta kuma taimaka wajen tabbatar da shari’ar musulunci.

Kudirin ya samu sahalewa daga majalisar zartarwar jihar kuma ana shirin mika shi gaban majalisar wakilai don samun sahalewa.

Mai Alfarma sarkin musulmi ne zai zama babban shugaban hukumar da zarar shiri ya kammala kuma zai taimaka da shawarwari kan yadda kungiyar zata kawo ci gaba a jihar.

Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na jihar Sokoto ya shirya tsaf don kirkiro hukumar Hisbah saboda jin dadin al’umma, taimakawa gwamnati don rage ayyukan assha da sauran laifuka a jihar.

A wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai taimakawa gwamnan bangaren watsa labarai, Muhammad Bello, an jiyo cewa kwamishinan shari’a kuma alakalin alkalai, Sulaiman Usman ya na cewa “dokar ta kuma bukaci a samar da kujerar babban shugaban hukumar Hisbah.”

Da ya ke zantawa da manema labarai bayan taron kwamitin zartarwar jihar a ranar Laraba, alkalin alkalan ya ce, sarkin musulmi, mai alfarma Sa’ad Abubakar ne zai zama babban shugaban hukumar idan an kammala shirye shirye.

Ya ce, za a bawa sarkin musulmin mukamin ne saboda ci gaba da kuma martabar hukumar Hisbah.

Ya ce sarkin musulmin zai dinga jagorantar hukumar a taron karshen shekara tare da bada shawarwari kan yadda za su dinga gudanar da aikin su.

“Bayan kirkirar hukumar, kudirin kuma ya na tafe da karin dokoki uku.

“Na farko, dokar ta bawa alkalin alkalai damar naɗa kwamitin bincike a duk lokacin da bukatar hakan ta taso, da kuma bawa hukumar damar binciken manyan laifuka.

“Gwamnatin jihar a kokarin ganin an tabbatar da shari’ar musulunci, tabbatar da da’a da zaman lafiya, da kuma taimakawa jami’an tsaro wajen wanzar da zaman lafiya, akwai bukatar Musulmi su bi koyarwar musulunci da dokokin Allah (SWT) a Qurani na al-amru bil maarufi, wan nahyu anil munkari (umarni da kyakkyawa da hani ga mummuna a cikin al’umma).”

Malam Usman ya ce majilisar zartarwar ta amince da kudirin kuma za a mika shi gaban majalisa don samun sahalewa.

Ya ce hakan zai samar da kyakkyawan ci gaba ga jihar Sokoto da Najeriya da ma duniya baki daya.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here