Muna Iyakar Bakin Kokarinmu – Shugaban Majalisar Dattawa

 

Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan ya ce suna iyakar kokarinsu

A cewarsa kullum cikin zarginsu ake yi da gyara aljihunsu kuma a gaskiya ba hakan bane.

Ya ce sun fi duk wasu ma’aikatan gwamnati taka tsan-tsan, kuma suna bukatar addu’a.

Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, ya ce ‘yan majalisar dattawa ba kansu suke yi wa aiki ba, jaridar The Cable ta wallafa.

Yayin da Lawan yake jawabi a wani taro a majalisar ranar Laraba, ya ce ‘yan majalisar dattawa suna sane da abubuwan da suke yi.

A cewarsa, ‘yan majalisar sune wadanda suka fi saukin zuwa garesu cikin wadanda aka zaba.

“Wajibi ne a yi zaben gaskiya da gaskiya a 2023, kuma dole mu mayar da hankali. Idan kun gano wani abu wanda ya dace a yi, ku taimaka ku sanar damu. Kada ku dinga jira mu yi kuskure, sai ku fara fallasawa, kuna cewa wadannan aljihunsu kawai suke gyarawa.

“Daga dan zamana, na fahimci cewa ‘yan majalisar nan ba kansu suke yi wa aiki ba. Kuma wannan majalisar tana daya daga cikin wuraren da suka fi taka tsan-tsan.

“Duk abinda za mu yi sai mun bayyana shi, sannan an fi samun damar zuwa wurinmu,” yace.

Ya ce za a yi gyara a kan kundin tsarin mulki kafin watanni 3 na farkon shekarar 2021 su wuce.

“Mutane za su iya sukarmu, ko kuma zarginmu da yin yadda muka ga dama. Amma muna yin iyakar kokarinmu” yace.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here