Jam’iyyar PDP Na Shirin Rasa Wasu Gwamnoni da Sanatoci

Jam’iyyar APC ta na zawarcin Jagororin adawa a shiyyar Kudu maso gabas.

Mai Mala Buni ya umarci ‘Yan APC su karkato da wasu Gwamnonin yankin.

APC ta na sa ran samun karin Gwamnoni da ‘Yan Majalisa kafin zaben 2023 Jaridar Punch ta ce jam’iyyar APC ta na hobbasa na ganin ta jawo hankalin wasu gwamnonin hamayya a yankin Kudu maso gabashin Najeriya.

Jam’iyyar APC mai mulki ta na zawarcin kusoshin adawar ne bayan maganar sauya-shekar gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi daga PDP.

Shugabannin rikon-kwaryan jam’iyyar APC, sun ba manyanta a kudu maso gabashin Najeriya umarni su karkato da hanlin manyan ‘yan hamayya.

APC a karkashin jagorancin Mai Mala Buni ta na neman samun karin yawan rinjaye a majalisar tarayya da iko a jihohi a yankin da PDP ta ke da karfi.

Daga cikin wadanda shugabannin APC su ke hari akwai gwamnan jihar Anambra, Willy Obiano da takwarorinsa Okezie Ikpeazu da Ifeanyi Ugwuanyi.

Jam’iyyar PDP ta fada wa jaridar cewa yunkurin ‘ya ‘yan APC ba ya tada mata hankali domin kuwa a karkashin PDP aka zabi wadannan gwamnoni.

PDP mai hamayya ta na ganin cewa nan ba da dadewa ba za a samu sauyin-sheka a jirgin APC.

Masu yi wa APC wannan kokari na rusa jam’iyyar PDP sun hada da gwamnan jihar Imo, Sanata Hope Uzodimma, Uzor Kalu da kuma Rochas Okorocha.

Wannan ya na cikin shirin da APC ta ke yi na ganin ta samu kuri’u masu tsoka a zabe mai zuwa na 2023.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here