Majalisar Dokokin Japan ta Nada Sabon Firaminista

 

Majalisar dokoki a Japan ta nada Fumio Kishida a matsayin sabon firaminista.

Mista Kishida, wanda ya dare shugabancin jam’iyyar masu sassaucin ra’ayi da ke mulki a makon da ya gabata, ya maye gurbin Yoshihide Suga, wanda gazawarsa a yaki da annobar corona ta janyo wa rasa mukaminsa.

Majiyoyin da ke kusa da sabon firaiministan sun ce yana da niyyar gudanar da babban zabe a karshen wannan watan, tun ma kafin lokacin da ake hasashe.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here