‘Yan Ta’addan Boko Haram Sun Kayyade wa Iyaye Cewa su Dinga Aurar da Yara Mata a Shekaru 12 a Jahar Neja

 

‘Yan ta’addan Boko Haram sun kwace mulki a wasu yankunan jahar Neja inda suka koma hukuma baki daya.

‘Yan Boko Haram sun tattara jama’ar yankin inda suka kayyade wa iyaye cewa a shekaru 12 za su dinga aurar da yara mata.

An gano cewa, a Awulo, Kuregbe da Kawure, ‘yan ta’addan ne ake kai wa kara ko da kuwa rikicin cikin gida ne sai su yi sasanci.

Shiroro, Niger – ‘Yan ta’addan Boko Haram sun addabi jama’a mazauna karamar hukumar Shiroro ta jahar Neja da su dinga aurar da ‘ya’yansu mata a shekaru 12.

Daily Trust ta rawaito cewa, mazauna yankin da lamarin ya shafa sun ce ‘yan ta’addan sun ba su umarnin cewa kada su kuskura su saurari wata hukuma.

Daya daga cikin mazauna yankin kuma daga cikin matasan Shiroro mai suna Bello Ibrahim, ya sanar da Daily Trust cewa:

“A wani lokaci, suna kauyen Kawure, kauyen tsohon sanata mai wakiltar Niger ta gabas, David Umaru.

“Amma dakarun sojoji sun fatattake su bayan ayyukan rundunar hadin guiwa. Sai dai kuma, bayan wani lokaci, sun sake komawa saboda babu sansanin sojoji a wurin.

“Toh a yanzu, ba a Kawure kadai su ke ba, sun bazu har zuwa yankunan da suka hada da Kuregbe, Awulo da sauransu.

“A Awulo da kuma yankin Kuregbe, sun tattaro jama’a Musulmi da Kirista kuma sun ba su umarnin aurar da ‘ya’yansu mata a shekaru 12.

“Babu wata doka a yankin baya da ta Boko Haram. Idan mazauna yankin suna da wata matsala ko da ko ta cikin gida ce, su ake kai wa kara domin sasanci.

“Babu wani korafi da ake kai wa ‘yan sanda ko kotu ko kuma wata hukuma domin sasanci.”

Wani mazaunin yankin ya ce ‘yan ta’addan na rayuwarsu a sake.

A cewarsa:

“Suna al’amuran rayuwarsu kamar kowa kuma a sake suke rayuwa da ‘yan kauyen. Sun zama hukuma a kauyukan. A Kawure, Awulo da Kuregbe ne suka da sansanoninsu. Su na tirsasa mazauna yankunan wurin yi musu biyayya.

“A dukkan gundumomin Chukuba da Kuregbe, babu wasu ‘yan fashin daji, ‘yan Boko Haram ne zalla.”

Shugaban karamar hukumar Shiroro, Suleiman Chukuba ya tabbatar da tururuwar da ‘yan Boko Haram ke yi a yankin. Ya ce gundumomi hudu ne lamarin ya shafa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here