Gwamnan Jahar Borno ya yi wa Malaman Makaranta Jarrabawar Bazata
Gwamnan Borno, Babagana Zulum ya ziyarci wata makaranta a garin Baga.
Farfesa Babagana Zulum ya yiwa malaman makarantar jarrabawar musamman.
Zulum yace babu malamin da za a kora a sakamakon wannan gwaji da ya yi.
Borno – Mai girma gwamnan jahar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya shirya wata jarrabawar ba-zata ga malaman makaranta a garin Baga.
Kamar yadda hadimin gwamnan, Isa Gusau ya fada, Farfesa Babagana Umara Zulum ya yi hakan ne domin ya gane ilmi da kwarewar wadannan malamai.
Gwamnatin Borno za ta kori malamai daga aiki?
Gwamna Babagana Umara Zulum ya ce bai yi wannan jarrabawa da nufin ya kori wani malami daga aki ba, sai dai domin sanin inda ya kamata a tura su.
“Wadanda ba su da kokarin koyar wa za su samu zabi; ko dai a sauya masu wurin aiki zuwa ofisoshin gwamnati, ko a kai su inda za a kara ba su horo.”
Read Also:
“Zulum yace a karshen duk shekara, gwamnati za ta auna kowane malami da ‘dalibansa, a taimaka masu da wurin zama da abubuwan da su ke bukata.”
Zulum ya yi wa Malamai goma ta arziki
“Bayan tattauna wa da bayyana sakamakon jarrabawa da aka yi, Zulum ya bada sanarwar kyautar N20, 000 da yadi goma na shadda ga kowane malami.”
“Shugaban makarantar sakandaren da shugaban malaman firamare sun samu N50, 000 da yadi goma.”
Gwamnan ya fada wa malaman cewa muddin za su rika taimaka wa al’umma, gwamnati za ta ba su goyon-baya, har ta kara wa wadanda suka dace albashi.
Zulum ya ce idan ya sake ziyartar garin Baga, zai kira malami da sunan shi, ya auna kaifin basirarsa da ta daibansa, tare da alkawarin tallafa wa dalibai.
Jaridar Daily Trust ta ce an shirya wa malaman jarrabawar ne a ranar Talata, 10 ga watan Agusta, 2021.
Za a ga gwamnan shi kadai ya na sa ido yayin da ake jarrabawar. Farfesan ya tambayi malaman bayani a game da kansu, sannan ya jefa masu wasu tambayoyi.