NIS da NSCDC: Ta Sanar da Ranar Jarrabawa

Ma’aikatar harkokin cikin gida ta sanar da cewa za ta gudanar da jarrabawa daukan aiki a hukumominta guda biyu.

Wadanda suka nemi guraben aiki a karkashin hukumomin sun dade suna jiran sanarwar lokacin rubuta jarrabawar.

Ogbeni Rauf Aregbesola, ministan ma’aikatar harkokin gida ya dauki alkawarin cewa za’a tabbatar da adalci da daidaito wajen daukar sabbin ma’aikatan.

Gwamnatin tarayya, a ranar Litinin, ta sanar da cewa ta tsayar da ranakun 7 da 8 ga watan Disamba a matsayin ranakun rubuta jarrabawar daukan aiki a hukumar kula da shige da fice (NIS) da rundunar tsaro ta NCSDC (Nigerian Security and Civil Defence Corps).

Fiye da ‘yan Najerya miliyan biyu ne suka nuna sha’awar samun gurbin aiki a hukumomin guda biyu da ke karkashin ma’aikatar harkokin cikin gida.

A cikin wani jawabi da Alhaji Mohammed Manga, darektan yada labarai a ma’aikatar harkokin cikin gida, ya fitar, ya ce ma’aikatarsu ta hada kai da hukumar shirya jarrabawar shiga manyan makarantu (JAMB) wajen gudanar da jarrabawoyin.

Alhaji Manga ya bayyana cewa za’a gudanar da jarrabawar ta hanyar amfani da tsarin amsa tambayoyi a na’ura mai kwakwalwa (Computer-Based Test; CBT) domin tabbatar da adalci da dakile magudi da alfarma.

Ya ce sun hada gwuiwa da hukumar JAMB ne domin bayar da dama ga dukkan wadanda suka nemi guraben aiki a hukumomin biyu.

A ‘yan kwanakin baya bayan nan ne ministan harkokin cikin gida, Ogbeni Rauf Aregbesola, ya sanar da cewa ma’aikatarsa za ta tabbatar da adalci da daidaito wajen daukar sabbin ma’aikatan.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here