Gwamnonin Arewa Sun Fadi Dalilin Amfani da Sojojin Haya

 

Bukatar amfani da sojojin haya wajen yaki da Boko Haram ya samu goyon baya daga shahararrun mutane.

Musamman, gwamnoni daga arewa maso gabas sun rungumi wannan kira wanda Gwamna Zulum ya fara yi.

A cewarsu, ta hakan ne kadai za a iya yin nasara a yaki da ake yi da yan ta’adda.

Gwamnonin Arewa maso gabas sun goyi bayan kira ga gwamnatin tarayya a kan tayi amfani da sojojin haya wajen yaki da ta’addanci a yankin.

Gwamnan jihar Taraba, Darius Ishaku, ya bayyana hakan a ranar Talata, 1 ga watan Disamba, a madadin takwarorinsa a yayin wata ziyara da ya kai jihar Borno don yi wa gwamnati da mutanen jihar jaje.

Legit.ng ta tattaro a baya cewa mayakan Boko Haram sun kai wani mummunan hari kan manoma a garin Zabarmari wanda yayi sanadiyar rasa akalla rayuka 43.

A cewar Darius, gwamnonin na goyon bayan shawarwarin da Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno ya bayar, kan yadda za a yi nasara a yaki da mayakan Boko Haram a yankin.

Ya dan uwanmu, mun zo nan ne domin yi maka ta’aziyya kan kisan manoma da yan ta’addan Boko Haram suka yi; shakka babu mun yi bakin ciki da juyayi,” in ji Ishaku.

Ya kara da cewa: “Zan yi magana kan bukatarka, wanda ka bayyana cewa ya kamata gwamnatin tarayya ta gayyaci sojojin haya su zo su taimaka mana a wannan matsalar saboda abunda ba za ka iya ba, abunda ba za ka iya magancewa ba, ina ganin ya kamata mu gayyaci wadanda za su iya magance mana matsalar.”

Baya ga gayyatar sojojin haya, Gwamna Zulum ya nemi a kwashi matasa aiki a rundunar soji domin bunkasa karfinsu, sannan a samar da kayayyakin aiki na zamani.

A yayin ziyarar ranar Talata, Gwamna Ishaku ya ce: “Ba za mu iya ci gaba da jimami ba, dole a samu lokacin kawo karshen wannan juyayin.

“Dukkaninmu a kungiyar gwamnonin arewa maso gabas, muna rokon gwamnatin tarayya da ta sami mafita a kan lamarin Boko Haram.”

Gwamnan na Taraba ya kuma roki gwamnatin tarayya da ta yi duba cikin lamarin tabarbarewar abubuwan more rayuwa a yankin sannan ta bashi kulawar da yake bukata.

A cewarsa, abun kunya ne cewa arewa maso gabas na samun kudaden shiga na 0.35% a kasafin kudin kasar duk da matsalolin ta’addanci a yankin, Channels TV ta ruwaito.

Gwamna Zulum, a martaninsa ya mika godiya ga ziyarar da tawagar ta kawo masa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here