Jam’iyyar AAC Reshen Jihar Akwa Ibom ta Kaddamar da Jarumar Fim a Matsayin Mataimakiyar Gwamna

Jam’iyyar African Action Congress (AAC) ta kaddamar da jarumar Nollywood, Caroline Hutchings aka Caroline Danjuma matsayin mataimakiyar gwamna a Akwa Ibom.

Caroline Danjuma ta shiga jerin sauran jaruman fina-finai irinsu Tonto Dikeh da Funke Akindele wadanda suma aka zabe su yan takarar mataimakan gwamna a wasu jam’iyyu a zaben 2023.

A sanarwar da ta fitar, AAC ta ce an zabi Caroline ne saboda kaunar mutane da ta ke yi, rayuwa ta gari da jajircewarta wurin inganta garuruwa a Akwa Ibom da iya jagoranci.

An kaddamar da Jaruma Coroline Hutchings wanda aka fi sani da Caroline Danjuma a matsayin abokiyar takarar Mr Iboro Otu, dan takarar gwamna na jam’iyyar African Action Congress (AAC) a zaben 2023 a Akwa Ibom, Daily Trust ta rahoto.

Jarumar ta shiga jerin sauran jaruman fina-finan kudu kamar Funke Akindele (PDP) da Tonto Diike (ADC) da suka zama mataimakan gwamna a zaben na 2023 da ke tafe.

Jarumai ta zama mataimakiyar shugaban kasar ne a jam’iyyar da dan jarida kuma mai rajin kwato hakkin bil-adama, Omoyele Sowore ya kafa.

Dalilin da yasa AAC ta zabi Caroline

A sanarwar da jam’iyyar ta fitar mai dauke da sa hannun shugabanta na jiha da sakatare, Utip Etiebet da Gabriel Ekpo, AAC ta yi bayanin cewa an zabi Caroline ne saboda kaunar mutane da ta ke yi, rayuwa da ta dace da jajircewarta wurin inganta garuruwa a Akwa Ibom da iya jagoranci.

Wani sashi na sanarwar:

“A madadin jam’iyyarmu, ta African Action Congress da kungiyar yakin neman zaben gwamna na Iboro Otu, muna son sanar da yan jam’iyyar mu da mutanen Akwa Ibom da yan Najeriya yar takarar mataimakiyar gwamnan mu a zaben 2023 a zaben Jihar Akwa Ibom, Cif Mrs Caroline Uduak Danjuma.

“Cif Mrs Caroline, Obong Uwana na Eket, yar kasuwa ce na kasa da kasa, jarumai wacce ta lashe lambobin yabo kuma mai taimakon alumma. Ta fito ne daga gidan basarake, Mai martaba, Edidem William Esiet Ekwere.”

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here