Jarumar Kasar Ghana ta Karbi Addinin Musulunci

 

Jarumar kasar Ghana mai suna Akuapem Poloo ta bar addinin Kirista inda ta karbi Musulunci.

Poloo da kanta ce ta sanar da labarin Musuluntar tata a shafinta na soshiyal midiya.

Masoya da mabiyanta sun tayata murnar karbar kalmar shahada da ta yi sannan sun yi mata fatan alkhairi a sabon addininta.

Shahararriyar jarumar kasar Ghana Rosemond Alade Brown wacce aka fi sani da Akuapem Poloo, ta karbi addinin Musulunci.

Poloo ta Musulunta ne a ranar Talata, 9 ga watan Agusta, bayan ta yi kalmar shahada tare da kadaita Allah.

Jarumar da kanta ce ta sanar da labarin Musuluntar tata a shafinta na Instagram inda ta wallafa hotunan dan kwarya-kwaryan taron da aka shirya na Musuluntarta tare da wasu malamai.

Tuni mabiyanta suka shiga sashin sharhi domin tayata murna tare da yi mata barka da zuwa cikin addinin Musulunci.

Ga yadda ta rubuta a shafin nata:

“Alhamdulillah na zama cikakkiyar Musulma yanzu godiya ga mataimakin limamin ASWAJ Ga West da babban limamin Nsakina Quran Reciter da ahlinsa kan taimakawa da suka yi wajen yiwuwar hakan ”

Jama’a sun yi martani a kan wannan ‘karuwa da Musulunci ta samu

madam__korede

“Masha Allahu Barka da zuwa addinin Islama❤️❤️❤️❤️ Allah ya albarkace ki yar’uwa”

kalsoume ta rubuta:

“Alhamdulillah ❤️”

osmanstarsking082 ya ce:

“Allah Ya albarkace ki a sabon addininki ❤️ barka da zuwa Islam ”

keimadimmuah ta ce:

“Ina tayaki murna ❤️❤️❤️❤️”

mufadilhamda ta ce:

“❤️Mash Allah ina taya ki murna ❤️❤️”

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here