Rashin Tsaro: Mambobin Majalisar Dokokin Katsina Zasu Gana da Shugaba Buhari da Gwamna Masari

 

Mambobin majalisar dokokin jihar Katsina zasu gana da gwamna Masari da shugaba Buhari kan rashin tsaron jihar.

Majalisar ta cimma wannan matsaya ne yayin da matsalar tsaro ke ƙara taɓarɓarewa a jihar, mahaifar shugaban kasa.

Wani rahoto ya nun mutane sun fara tashi daga wasu anguwanni a cikin birnin Katsina saboda tsoron kawo hari.

Katsina – Majalisar Dokokin Jihar Katsina ta cimma matsayar gana wa da gwamna Aminu Bello Masari, da shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, kan yanayin taɓarɓarewar matsalar tsaro a jihar.

Shugaban kwamitin yaɗa labarai na majalisar, Alhaji Ali Abu Al-Baba, shi ne ya bayyana haka ga manema labarai ranar Talata a Katsina, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Al – Baba ya bayyana cewa majalisar ta damu matuƙa kan karuwar rahoton ayyukan yan bindigan daji a sassan jihar, wacce take mahaifar shugaban kasa.

A cewar ɗan majalisar, kalubalen tsaron da ake fama da shi yanzu haka a jihar babban abun damuwa ne kuma bai kamata a zuba masa ido ba.

Bugu da ƙari ya ce mambobin majalisar zasu tafi kai tsaye su gana da shugaban kasa game da bukatar dake da akwai na lalubo hanyoyi da ɗaukar matakan kawo karshen ayyukan yan bindiga.

A jawabinsa, Honorabul Al- Baba ya ce:

“Wajibi a gaggauta yin wani abu domin dakile ta’addancin yan bindiga. Saboda haka muna rokon samun goyon baya da kuma haɗin kan kowa da kowa a yaƙi da masu tada ƙayar baya.”

A halin yanzun, mambobin majalisar dokokin sun nuna goyon bayan su ga kiran gwamna Aminu Masari, wanda ya nemi al’umma su farka daga bacci, su mallaki makaman kare kan su daga yan ta’adda.

latest nigerian newspapers headlines today

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com