Sean Connery: Jarumin Shirin James Bond ya Mutu
Jarumin min nan da ya fito a fina-finan James Bond, Sean Connery, ya mutu yana da shekara 90 da haihuwa.
Jarumin, wanda ɗan asalin Scotland ne a Birtaniya, ya yi fice a fim ɗin James Bond kuma ya shafe sama da shekara 50 a masana’antar fim ana gwagwarmaya da shi.
Rahotanni sun bayyana cewa Mista Connery ya mutu ne a cikin baccinsa a Bahamas bayan ya shafe lokaci mai tsawo ba shi da lafiya.
Wasu daga cikin fina-finan da ya yi da suka yi fice sun haɗa da The Hunt for Red October da Highlander da Indiana Jones and the Last Crusade, sai kuma The Rock.
Sean Connery ya lashe kyautar Oscar a 1988 sakamakon irin rawar da ya taka a fim ɗin The Untouchables.
Ɗan marigayin, Jason Connery ya bayyana cewa sai da mahaifinsa ya gayyaci ‘yan uwansa da yawa zuwa ƙasar Bahamas suka zo wurinsa, inda a dare ɗaya ya mutu.
Fim ɗin asali na James Bond
Sir Sean, wanda aka haifa a Fountainbridge da ke Edinburgh, ya fara taka rawa a fim ɗin James Bond na Dr No a 1962, inda bayan nan ya yi wasu guda shida da suka haɗa da From Russia with Love da Goldfinger da Thunderball da You Only Live Twice.
Bayan nan kuma sai ya yi fim ɗin Diamonds Are Forever da kuma Never Say Never Again.
Mutane da dama na cewa shi ne wanda ya fi ƙwarewa ko kuma dacewa da 007, wanda shi ne tauraro a fim ɗin.
Sarauniyar Ingila ta ba shi kyautar girmamawa a shekarar 2000.
Masu shirya fim ɗin na James Bond, Michael G Wilson da kuma Barbara Broccoli sun ce sun kaɗu bayan jin mutuwar jarumin.
Sun bayyana cewa: “Ana ci gaba, kuma za a ci gaba da tunawa da shi a matsayin asalin wanda ya fara taka rawa a fim ɗin James Bond.”
Sun kuma bayyana cewa ya bayar da gudunmawa matuƙa wurin ganin cewa wannan fim ɗin ya samu karɓuwa, haka kuma sun ce za su ci gaba da gode masa har abada.
Sir Sean, na ɗaya daga cikin masu goyon bayan Scotland ta samu ‘yancin kai, inda a wata hira da aka yi da shi ya ce zai iya barin gidansa da ke Bahamas domin ya koma Scotland ya ci gaba da zama idan ta zaɓi ta ɓalle daga Birtaniya