Jawabin Atiku Abubakar a Wurin Taron Gabatar da Okowa
Ba a ga jigon jam’iyyar PDP kuma gwamnan Jihar Rivers, Nyesom Wike, a bikin gabatar da takwararsa na Jihar Delta, Ifeanyi Okowa, a matsayin dan takarar mataimakin shugaban kasa na PDP a zaben 2023, rahoton Leadership.
Idan za a iya tunawa Wike na ya zo na biyu a zaben fidda gwani na shugaban kasa na PDP da aka yi a ranar 28 na watan Mayu inda ya samu kuri’u 237 yayin da Atiku ya samu kuri’u 371.
Tun bayan zaben fidda gwanin, ana ta hasashen cewa Wike ne zai zama dan takarar mataimakin shugaban kasa ga Atiku saboda karfin kafa aji da ya ke da shi a jam’iyyar.
Read Also:
Amma, Okowo ne aka gabatar a matsayin dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar ta PDP inda jiga-jigan jam’iyyar suka hallara a hedkwatarta a Abuja.
Ya ce wani abu da aka duba wurin zaben Okowa shine dacewarsa ya zama magajinsa idan an zabe shi shugaban kasa a 2023
Jawabin Atiku Abubakar wurin taron gabatar da Okowa
“Na yi murnar sanar da Gwamna Ifeanyi A. Okowa a matsayin mataimaki na. Ina fatan jagorancin kasar mu tare, tare da yan Najeriya don gina gaba mai kyau gare mu baki daya,” in ji Atiku.
Baya ga shugaban jam’iyyar na kasa Dr Iyorchia Ayu, mambobin kwamitin ayyuka, NWC, mambobin kwamtin amintattu, BOT, jiga-jigan jam’iyyar da takwarorin Okowa sun hallarci taron.
Sun hada da gwamnonin jihohin Enugu, Ifeanyi Uguanyi, Bauchi, Bala Mohamemd; Akwa Ibom, Udom Emmanuel; Edo, Godwin Obaseki, da Benue; Samuel Ortom.
Saurari karin bayani …