Jawabin Shugaba Buhari Kan Rufe Iyakoki
Shugaba Buhari da mambobin kwamitin bawa shugaban kasa shawar a kan bunkasa tattalin arziki.
A jawabin da ya gabatar, shugaba Buhari ya bayyana cewa gwamnatin za ta yaki hauhawar farashin kayan abinci a shekarar 2021.
Kazalika, ya shawarci ‘yan Nigeria su rungumi doma tare da daina dogaro da samun arziki daga man fetur.
A ranar Talata ne shugaba kasa, Muhammadu Buhari, ya bayyana cewa rufe iyakokin Nigeria ya taimaka wajen kare kasa daga shiga wasu manyan matsaloli.
Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne a Abuja yayin taronsa da kwamitin da ke bawa shugaban kasa shawara a kan harkokin da suka shafi tattalin arziki.
A cikin watan Agusta na shekarar 2019 ne gwamnatin tarayya ta bayar da umarnin rufe iyakokin Nigeria na kan tudu.
Read Also:
Sai dai, daga bisani, shugaba Buhari, a ranar 16 ga wata Disamba, ya bayar da umarnin a bude hudu daga cikin iyakokin daga ranar 31 ga watan Disamba.
Yayin taronsa da mambobin kwamitin, Buhari ya umarci babban bankin kasa (CBN) akan kar ya sake ya fitar da wani kudi domin shigo da kayan abinci.
“Ba don mun rungumi noma, mun rufe iyakokinmu ba, da mun shiga mawuyacin halin da yafi na yanzu.
“Za mu cigaba da bayar da tallafi da gudunmawa domin bunkasa harkar noma, dole mu karfafawa jama’a gwuiwa su koma gona.
“Dole mu koma ga arzikinmu, mu daina tunanin cewa kudaden man fetur zasu azurta mu.
“Yanzu jama’a sun fara komawa gona, ya kamata mu yi amfani da wannan dama domin saukakawa kanmu rayuwa,” a cewar Buhari.
Kazalika, shugaba Buhari ya jaddada muhimmanci da tasirin bangaren noma wajen raya tattalin arzikin kasa.