Jawabin Wani Mutum da ‘Yan Bindiga Suka Saki

 

Wani da ya fada hannun ‘Yan bindiga ya bada labarin abin da ya faru da su.

Wannan mutumi ya ce an bukaci 50m a hannunsa, amma N4m ta fito da shi.

Da yake tsare, wannan mutum ya hadu da Malamin ABU Zaria da aka dauke.

Wani mazaunin jihar Kaduna da ya yi tsawon kwanaki 12 a hannun masu garkuwa da mutane ya bayyanawa jaridar Daily Trust irin abin da ya faru da shi.

Wannan Bawan Allah ya bada labarin yadda ya hadu da malamin jami’ar ABU Zaria, Dr. Ibrahim Bako, wanda aka tsare a lokacin (yanzu ya samu ‘yanci).

“Ina tafiya ni kadai a cikin mota a hanyar Kaduna-Birnin Gwari, bayan an wuce Buruku, kusa da Rumanan Gwari, sai ‘yan bindiga su ka bude mani wuta.”

A cewarsa, daga nan aka dauke shi zuwa cikin daji, su ka yi tafiyar kusan kilomita uku, sai su ka hau babur, su kayi doguwar tafiya zuwa inda aka tsare su.

A nan ne fa aka yi wa wannan mutumi tare da sauran wadanda aka kama mummunan bugu domin su yi maza su fadi abubuwan da su ka mallaka a Duniya.

A game da adadin ‘yan bindigan, sai ya ce: “Su na da yawa, sun haura 20, akwai manya da kananansu.”

Sun ce mani: “Idan gwamnati suna son zaman lafiya, dole su gane cewa su ‘Yan Najeriya ne, sai jami’an tsaro su yi sulhu da su, amma ba a rika kiransu miyagu ba.”

Daga cikin wadanda aka kashe akwai wanda aka gaza samun lambar wayar ‘yanuwansa, akwai kuma wanda ya yi masu tayin N10, 000 domin a sake shi.

Farfesan da aka sace a ABU Zaria yana cikin wadanda wannan mutumi ya hadu da su a dajin. ‘Yan bindigan sun ki karbar N2m, su ka rantse sai an basu N10m.

Tun ana cewa a kawo miliyan 50, aka yi ta magana har aka zo kan miliyan 4, ‘yanuwan wannan mutumi su na bada wannan kudi, aka fito da shi, aka sake shi.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here