Bayan Nadi: Jawabin Sabon Sifeto Janar na ‘Yan Sanda, IGP Usman Alkali
Sabon sifeta janar na ‘yan sanda ya ce shugabancinsa zai baiwa ‘yan sanda damar gyara matsalar tsaron Najeriya.
IGP Usman Alkali ya bayyana hakan ne a ranar Laraba bayan farfesa Osinbajo ya nada shi a gidan gwamnati dake Abuja.
A cewarsa, zai fifita kuma ya tabbatar da an samar da ‘yan sandan yanki don kawar da matsalolin tsaron dake addabar al’umma Sabon sifeta janar na ‘yan sanda, Usman Alkali ya ce ‘yan sanda a karkashin mulkinsa zasu tabbatar da bunkasa harkar tsaro a Najeriya.
Ya kara da bada tabbacin fifitawa da kuma tabbatar da ‘yan sandan jahohi a karkashin mulkinsa.
Read Also:
IGP ya bayyana hakan ne a gidan gwamnati dake Abuja bayan mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya nada shi.
Shugaba Muhammadu Buhari ya daura Alkali a kujerar sifeta janar na ‘yan sandan Najeriya, inda ya maye gurbin Mohammed Adamu wanda ya kamata ya sauka daga madafin iko a watan Fabrairu, saidai an kara masa watanni 3. Saidai Adamu bai karasa watanni ukun ba.
Alkali yace dama akwai tsarin ‘yan sandan yankin tun baya, sai dai ba a aiwatar dashi ba, ya ce mulkinsa zai tabbatar da hakan.
‘Yan Najeriya da dama sun dade suna kira akan tabbatar da ‘yan sandan yankuna a kasar nan.
Sun yarda da cewa hakan zai taimaka wurin shawo kan matsalolin tsaro da suka addabi bangarori da dama na kasar nan.
A matsayin daya daga cikin hanyoyin magance matsalar tsaro, kwanan nan gwamnatin tarayya ta amince da bayar da N13,300,000,000 don fara tabbatar da tsarin ‘yan sandan yanki.