Jawabin Sabon Shugaban Rikon ƙwarya na Ribas Bayan Rantsar da Shi

 

Abuja – Sabon shugaban riko na Ribas, Vice Admiral Ibok-ete Ibas (mai ritaya), ya bayyana kudirinsa na tabbatar da doka da oda a jihar da ke fama da rikici.

Vice Admiral Ibas ya ce zai yi duk mai yiwuwa wajen tabbatar da tsaro, bin doka da daidaito a jihar Ribas da ke fama da rigingimu da suka ƙi ci suka ƙi cinyewa.

Tinubu ya rantsar da shugaban riƙon Ribas

Shugaban rikon ya yi wannan jawabi ne da yake zantawa da masu ɗauko rahoto a fadar shugaban ƙasa bayan ganawa da Shugaba Bola Ahmed Tinubu, cewar rahoton Channels tv.

Shugaban ƙasa, Bola Tinubu ya rantsar da tsohon hafsan rundunar sojin ruwa ta Najeriya, Ibas a matsayin shugaban riko wanda zai kula da lamurran Ribas na wani lokaci.

Jim kaɗan bayan karɓar rantsuwar kama aiki a fadar shugaban kasa, Vice Admiral Ibas ya yi alkawarin tabbatar da tsaro a Ribas.

Jawabin da Ibas ya yi bayan rantsuwa

“Mun fahimci yanayin da ya kawo mu wannan matsayi kuma mai girma shugaban ƙasa ya yi bayanai a jawabin da ya yi kai tsaye.

“Idan batun da ke gabanmu shi ne tabbatar da doka da oda a jihar, to wannan ne aikin da ya rataya a kaina ko zan tasa shi domin kowanne irin ci gaba ya samu a Jihar Ribas.

Tsohon hafsan rundunar sojin ruwa ya yi alkawarin yin aiki tare da sauran masu ruwa da tsaki don tabbatar da zaman lafiya, tsaro, da kwanciyar hankali ga al’ummar jihar Ribas da Najeriya baki daya.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here