Jawabin Shugaba Tinubu a Wajen Gabatar da Kasafin Kudin 2024
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya gabatar da kudurin kasafin kudinsa na farko ga zaman hadin gwiwar Majalisun Najeriya.
Kasafin kudin na 2024, wanda ya kunshi sama da naira tirliyan 27.5 zai fi mayar da hankali wajen karfafa tsaron kasa da samar da aikin yi da harkokin zuba jari da rage fatara a tsakanin al’umma.
Shugaba Bola Tinubu ya ce an tsara kasafin kudin na shekara mai zuwa ne bisa hasashen sayar da gangar man fetur daya a kan dala 77.96, da hako kiyasin ganga miliyan 1.78 ta man fetur a kullum. Sannan da dalar Amurka daya a kan canjin naira 750.
Kasafin kudin ya yi kudurin kashe naira tirliyan 9.92 a bangaren ayyukan yau da kullum. Sai kuma naira tirliyan 8.25 wajen biyan bashi, yayin da manyan ayyuka za su samu naira tirliyan 8.7.
Ga muhimman bayanai daga cikin jawabin kasafin kudin a takaice:
Sashen Ilmi
Read Also:
Bunkasa rayuwar dan’adam da ba da fifiko ga kananan yara a matsayinsu na ginshikin al’umma.
Magance tsoffin matsalolin da aka dade ana fama da su a bangaren ilmi, ta hanyar aiwatar da karin tsari don samar da kudi ga ilmi mai zurfi, ciki har da shirin bashin karatu ga dalibai wanda zai fara aiki daga watan Janairun 2024,
Tattalin arziki
Sassauta hauhawar farashi zuwa kashi 21.4% (a yanzu alkaluman hauhawar farashi sun kai kashi 27.33
Bunkasar tattalin arziki da mafi karanci kashi 3.76.
Jaddada kawance tsakanin gwamnati da ‘yan kasuwa ta hanyar bullo da tanade-tanaden da kamfanoni za su iya cin gajiyar aiwatar da manyan ayyuka a bangaren samar da makamashi da sufuri da sauransu.
Ranto kudi jimillar naira tirliyan 7.83 don cike gibin kasadin kudin 2024
An yi hasashen cewa gibin kasafin kudi a kan naira tirliyan 9.18 a 2024
Hasashen biyan basuka da kashi 45 na jimillar kudin shiga da Najeriya ke sa ran samu.