Jerin Sabbin Jihohi 31 da Majalisar Wakilan Najeriya ta Bayar da shawarar ƙirƙira
Kwamitin sake nazarin kundin tsarin mulkin Najeriya na majalisar wakilan ƙasar ya bayar da shawarar ƙirƙiro ƙarin sabbin jihohi 31 a ƙasar.
Mataimakin kakakin majalisar wakilan ƙasar, Hon.Benjamin Kalu ne ya bayyana haka lokacin da ya karanto wasiƙar kwamitin, a zaman majalisar da ya jagoranta yau Alhamis.
Idan aka amince da buƙatar adadin jihohin Najeriya zai kai 67.
Ga jerin sabbin jihohin da kwamitin ya bayar da shawarar ƙirƙira daga wasu jihohin ƙasar na yanzu:
Arewa ta Tsakiya
Benue Ala daga jihar Benue.
Okun daga jihar Kogi.
Okura daga jihar Kogi.
Confluence daga jihar Kogi.
Apa-Agba daga jihar Benue.
Apa daga jihar Benue.
Abuja dada babban birnin ƙasar.
Arewa maso Gabas
Read Also:
Amana daga jihar Adamawa.
Katagum daga jihar Bauchi.
Savannah daga jihar Borno.
Muri daga jihar Taraba.
Arewa maso Yamma
New Kaduna da daga jihar Kaduna State.
Gurara daga jihar Kaduna.
Tiga daga jihar Kano.
Kainji daga jihar Kebbi.
Ghari daga jihar Kano.
Kudu maso Gabas
Etiti daga duka jihohin yankin shida.
Adada daga jihar Enugu.
Urashi daga duka jihohin yankin shida.
Orlu daga jihar duka jihohin yankin shida.
Aba daga duka jihohin yankin.
Kudu maso kudanci
Ogoja daga jihar Cross River.
Warri daga jihar Delta.
Bori daga jihar Rivers.
Obolo daga jihohin Rivers da Akwa Ibom.
Kudu maso Yamma
Toru-ebe daga jihohin Delta da Edo da kuma Ondo.
Ibadan daga jihar Oyo.
Lagoon daga jihar Lagos.
Ijebu daga jihar Ogun.
Oke-Ogun daga jihohin Ogun da Oyo da kuma Osun
Ife-Ijesha daga jihohin Ogun Oyo da kuma Osun.