Shugaban JIBWIS ya Magantu Kan Kashe Matafiya Musulmai a Jos

 

Sheikh Jingir ya magantu kan yadda aka kashe wasu matafiya musulmai a garin Jos jiya Asabar.

Malamin ya bayyana kukansa, tare da kiran mutane a fadin Najeriya da su kwantar da hankulansu.

Ya kuma bukaci gwamnati da ta gaggauta daukar mataki kan wannan mummunan lamari da ya faru.

Jahar Filato – Shugaban Majalisar Malamai na Kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Ikamatis Sunnah (JIBWIS), Shiekh Sani Yahaya Jingir, ya yi kira ga Musulmi a fadin kasar nan da su kwantar da hankalinsu bayan kisan matafiya musulmai da aka yi a Jos ranar Asabar.

Ya yi wannan kira ne a wata hira da manema labarai ranar Lahadi a Jos, Daily Trust ta ruwaito.

An ruwaito a baya cewa, wasu matafiya musulmai 25 aka kashe a Jos, Jahar Filato, har yanzu ba a ga wasu da dama ba.

Ya ce duk da kisan yana da zafi da bakin ciki, amma bai kamata mutane su dauki doka a hannun su ba. Sai dai malamin ya bukaci a gaggauta kamawa tare da gurfanar da wadanda suka aikata laifin.

Sheikh Jingir ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta jaha da su tabbatar da adalci ga matafiyan da basu ji ba basu gani ba.

Ya ce:

“Wannan ba shi ne karon farko da aka kama matafiya Musulmi aka kashe su a kan manyan hanyoyi ba.

“Me ya sa mutane za su ci gaba da aikata irin wannan danyen aikin kuma su tafi salin-alin? ba daidai bane.

Sheikh Jingir, ya ce a duk lokacin da gwamnati ta kafa wani kwamiti da zai binciki wata matsala, da kyar za a yi wani abu game da sakamakon kwamitin, tare da fatan wadanda suka aikata wannan aikin ba za su tsira ba.

Babban malamin na addinin Musulunci ya yabawa dukkan hukumomin tsaro kan irin martanin da suka yi cikin gaggawa.

Ya ce:

“Na kuma yaba da kokarin Gwamna Simon Lalong, Gwamna Rotimi Akeredolu da Shugaba [Muhammadu] Buhari, don tabbatar da cewa lamarin bai yi nisa ba.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here