Firgicin Taliban: Shugaban Kasar Afghanistan ya Tsallaka Zuwa Tajiskistan

 

Shugaba Ashraf Ghani na kasar Afghanistan ya tsere daga kasar biyo bayan mamayar Taliban.

Rahotanni daga kasar na bayyana cewa, a halin yanzu, Kabul na cikin firgici yayin da Taliban ke kara kaimi a lardin.

Rahoto ya kuma bayyana cewa, shugaban tuni ya tsallaka zuwa Tajiskistan domin tsira da ransa.

Afghanistan – A kasashen ketare kuwa, shugaba Ashraf Ghani ya tsere daga Afghanistan yayin da Taliban ke dab da shiga birnin Kabul, a cewar babban mai shiga tsakani na zaman lafiya na kasar Abdullah Abdullah.

Abdullah, shugaban babbar majalisar sasantawa ta kasa, a wani faifan bidiyo a shafinsa na Facebook yana cewa:

“Tsohon shugaban na Afgahnistan ya bar al’umma.”

Wani babban jami’in ma’aikatar harkokin cikin gida ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa Ghani ya tafi ne zuwa Tajikistan.

Ficewar Ghani ta zo ne a yayin tattaunawar mika mulki cikin lumana bayan mayakan Taliban sun kewaye Kabul bayan da suka kwace manyan biranen larduna 34 na kasar cikin kasa da makonni biyu.

A halin da ake ciki, wani jami’in Taliban ya shaida wa Reuters cewa suna duba rahotannin ficewar Ghani daga kasar.

A ranar Lahadin da ta gabata, sojojin Taliban sun kewaye fadar mulkin Afghanistan, inda suka yi alkawarin cewa Taliban ta umarci mayakanta da su guji tashin hankali tare da bayar da kariya ga duk wanda ke son barin Kabul.

Kabul na cikin firgici yayin da mayakan Taliban ke kara kaimi

A yayin da kungiyar Taliban ke kara kaimi a Kabul, ana kara samun fargaba a tsakanin mutane da dama a Kabul babban birnin Afghanistan.

Farashin kayan masarufi sun yi tashin gwauron zabi yayin da da yawa ke kokarin cire dukkan kudadensu, in ji rahoton Al Jazeera.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here