Jiga-Jigan Jam’iyyar PDP Daga Arewacin Najeriya Sun Dage Kan Mika Tikitin Takarar Shugaban Kasa ga Yankin
Rashin jituwa na kunno kai a cikin Jam’iyyar PDP kan batun rigingimun rabon mukamai da ake fama da su.
Rahotanni sun ce jiga-jigan jam’iyyar PDP daga arewacin Najeriya sun dage kan mika tikitin takarar shugaban kasa ga yankin.
Jiga-jigan sun riga sun ɗauki matsayar kuma a shirye suke su matsa lamba ga jam’iyyar don ta amince da matsayin su.
FCT, Abuja – Rahoton da jaridar Tribune ta wallafa ya nuna cewa jiga -jigan arewa a jam’iyyar PDP, suna ta faman neman goyon baya don samun tikitin takarar shugaban kasa na jam’iyyar gabanin babban zaben 2023.
Read Also:
A cewar rahoton, shugabannin arewa a PDP sun gana a ranar Talata, 22 ga watan Satumba a Abuja don bayyana matsayinsu gabanin ganawar su da gwamnan jahar Enugu kuma shugaban kwamitin rabon takara na PDP, gwamna Ifeanyi Ugwuanyi.
A cewar wata majiya da aka nakalto a cikin rahoton, taron a karkashin tsohon ministan harkokin ‘yan sanda, Adamu Waziri ya samu halartar jiga-jigai 28 na babbar jam’iyyar adawa a fadin shiyyoyi uku da suka hada arewacin Najeriya.
Fiye da wakilai 6000 za su halarci babban taron PDP
A halin da ake ciki, jaridar Vanguard ta rahoto cewa sama da wakilai 6,000 za su hallara a Abuja don zaben sabon NWC a watan Oktoba na wannan shekarar, Gwamna Ahmadu Fintiri na Adamawa ya bayyana.
Fintiri wanda shi ne shugaban kwamitin shirya babban taron na kasa ya bayyana hakan ne a sakatariyar jam’iyyar, Abuja, a ranar Alhamis, 23 ga watan Satumba, jim kadan bayan kaddamar da kwamitocin kananan hukumomi 15 a wani biki da manyan jami’an jam’iyyar suka halarta.