Jigon APC ya Mutu a Hannun yan Bindiga
FCT, Abuja – Rasuwar Rauf Adeniji, babban jigon jam’iyyar APC, ta girgiza jam’iyyar da kasa baki ɗaya.
Adeniji ya kasance Daraktan Gudanarwa na jam’iyyar kafin sace shi wanda ya rasa ransa bayan sa’o’i kaɗan.
Jigon APC ya mutu a hannun yan bindiga
An bayyana cewa jigon APC ya mutu jim kaɗan bayan sace shi, amma sai kwanan nan ne aka gano hakan daga ‘dan uwansa.
Majiyoyi sun ce akwai yunkurin ɓoye bayani daga jami’an tsaro da jam’iyyar APC kan yadda aka sace Adeniji da yadda ya mutu a cikin daji.
Wani jigon jam’iyyar APC, Jamiu Olawumi, ya ce masu garkuwa sun zo da karyar cewa wani ya tsallaka katanga don su iya kutsa gidan.
Read Also:
Sun ce wai suna kokarin kama wanda ya shigo, amma sai suka farmaki mazauna gidan bayan an buɗe ƙofa.
Ya ce:
“Babu wanda ya san halin da suke ciki har sai da safiyar washegari aka samu gawar wata mace, matar dan uwansa.
“An kashe ta a cikin daji aka jefar da gawarta kusa da hanya, daga nan babu labarinsu har kwanan nan.”
Kudin fansa da masu garkuwa suka nema Olawumi ya ce radadin kashe matar Adesiyan a gabansa ne ya jawo mutuwar Rauf Adeniji, wanda ya mutu bayan awa uku, cewar rahoton Leadership.
Ya kara da cewa: “Adesiyan ne ya bada labari, ya ce tsananin tashin hankali da firgicin kisan matar ne ya jawo masa mutuwa bayan wasu sa’o’i.”
Olawumi ya ce masu garkuwa sun nemi kudin fansar N250m, amma gwamnatin tarayya ta hana biyan kudin ko kadan.
Ya ce bayan an ceto wadanda aka sace ne aka fahimci cewa Adeniji ya mutu tun makonni da dama da suka gabata.